Saudiyya za ta dauki ma’aikatan gidaje daga karin ƙasashen waje 8

    0
    573

    Ma’aikatar Albarkatun Jama’a da Ci gaban Al’umma ta Saudiyya ta sanya wasu ƙarin ƙasashe takwas cikin jerin ƙasashen da za ta ɗauki ma’aikatan gidaje.

    Da yake zantawa da Okaz/Saudi Gazette, kakakin ma’aikatar, Saad Al-Hammad, ya ce adadin kamfanonin ɗaukar ma’aikata masu lasisi a Masarautar Saudiyya ya kai kamfanoni 43, yayin da adadin ofisoshin daukar ma’aikata ya kai 1,215.

    Ma’aikatar na niyyar daukar ma’aikatan hidimar gidaje daga wasu kasashen Asiya da Afirka takwas a shekarar 2022, in ji shi.

    Al-Hammad ya ce ma’aikatar tana bakin kokarinta wajen ganin an rarraba ƴan ƙasashe daban-daban a ma’aikatan hidimar gidaje a Masarautar ta yadda wasu kasashe masu fitar da ’yan kwadago ba za su yi wani korafi ba ko matsawa kasuwar daukar ma’aikata ta Saudiyya lamba tare da kara kudin daukar ma’aikata a cikin gida.

    Al-Hammad ya jaddada mahimmancin wayar da kan ‘yan kasa kan rashin cin zarafin ma’aikatan gida kamar jinkirta albashi da kuma tsare fasfo din su a gidan yari.

    Ya kuma jaddada bukatar kammala kwangilar daukar ma’aikatan cikin gida ta hanyar Musaned portal na ma’aikatar domin kare hakkin bangarorin biyu da kuma kaucewa sabani.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here