Hukumar Alhazai Musulmi ta Jihar Legas ta shirya addu’a ta musamman domin tabbatuwa da nasarar Hajjin 2022.
Am shirya addu’ar ne a Masallacin Shamsi Adisa Thomas (SAT) Mosque, da ke Tsohuwar Sakateriya, GRA a Ikeja.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Taofeek Lawal ya fitar a yau Alhamis.
Ya ce an shirya addu’ar ne domin Allah Ya sa musulmai da ga ƙasashen waje a fadin duniya su samu damar zuwa Hajjin bana, bayan an samu tsaiko na shekaru 2 sakamakon annobar korona.
A cewar sanarwar, da ya ke jawabi a wajen addu’ar, Mai baiwa Gwamna Shawara kan Harkokin Addini, Alhaji Ahmad Abdullahi Jebe, ya yabawa duk shugabannin hukumar da malaman bita a bisa jajircewar su na ɗora jihar a kan matakin na gaba-gaba a harkar Hajji da Ummara a ƙasar.
A batun naɗin mukamai na hukumar, Jebe ya ce sai da gwamnati ta yi nazari ta binciko waɗanda su ka cancanta kuma su na da gogewa a ln harkokin Hajji da Ummara sannan a ka basu makaman.
Ya kuma baiyana fatan sa na cewa Allah zai karbi addu’ar da a ka yi domin samu a ke aikin Hajji a bana.