Masarautar Saudiyya ta sanar da haramta wa maniyyata sanye da gajeren wando shiga masallatan Harami biyu masu tsarki, wato Masjid al-Haram da ke Makkah da Masjid Al Nabawi a Madina.
Duk wanda aka samu ya saɓa wa wannan sabuwar doka, za a ci shi tarar shi Riyal 200 zuwa 500.
Umurnin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar, wacce a ka wallafa a shafinta na Twitter na Haramain Syarifain a ranar Juma’a.
A cewar mahukuntan Saudiyya, sanya gajeren wando a masallatai da cibiyoyin gwamnati bayan aiwatar da wannan sabuwar doka ya saɓawa tsarin zamantakewa.
Sai dai gwamnati ta yi karin haske kan cewa mazan da ke sanye da gajeren wando a wani gurin da ba masallaci ba, ba za a ɗauke su a matsayin keta alfarmar sanya tufafi na jama’a ba sai a masallatai.
An shigar da sabbin tarar ne jim kadan bayan ministan harkokin cikin gida na Saudiyya Yarima Abdulaziz Bin Saud Bin Naif ya bayar da sanarwar ga ministocin inda ya bukaci a yi sauye-sauye.