NAHCON ta umarci hukumomin alhazai na jihohi su fara shirin Hajjin 2022

0
427

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta umarci hukumomin alhazai na jihohi da su yi maza-maza su fara shirye-shiryen Hajjin 2022.

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, Zikrullah Kunle Hassan, shi ya bada umarnin a Abuja a yau Laraba yayin ganawa da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi a faɗin ƙasar nan.

Wannan matakin na NAHCON ya zo ne bayan da Hukumar ta samu umarnin hakan da ga Saudi Arebiya a kan fara shirye-shiryen Hajjin bana.

Hassan ya yi bayani cewa a bana, Hukumar Hajji da Ummara ta Saudiya ce za ta yi tsare-tsare da shirye-shirye na Hajji, ba kamar shekarun baya ba da hukumomin alhazai na ƙasashen waje ke shiga a yi shirye-shirye na kafin Hajji.

Shugaban NAHCON ɗin ya kuma umarci hukumomin alhazai na jihohi da su mayar da kuɗaɗen da alhazai su ka fara biya zuwa asusun adadin gata na Hajji da ke bankin jaiz domin a daidaita shirin na Hajjin 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here