Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta umarci hukumomin alhazai na jihohi da su maida kuɗaɗen ajiyar da maniyyata su ka biya zuwa asusun Adashin Gata na Hajji, wanda a ka fi sani da Hajj Savings Scheme.
Wannan umarnin na ƙunshe ne a wata sanarwar da Shugabar Sashin Hulɗa da Jama’a na NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a yau Litinin.
Ta ce NAHCON ta amince da yin amfani da adashin gata ɗin ne domin maida harkar biyan kuɗaɗen ta bai ɗaya da kuma gaskiyar cewa wata kafa ce ta tabbatar da yin gaskiya da amana.
A cewar Usara, an yi ittifakin cewa adashin gata ɗin wata hanya ce ta tabbatar da gaskiya ga maniyyata.
Sanarwar ta kuma baiyana cewa Hukumar alhazai tabbatar da cewa hukumomin alhazai na jihohi za su ci gaba da kula da walwalar alhaxai yadda a ka saba sai dai idan an samu canji da ga Saudiya.
A sanarwar, NAHCON ta yi kira ga hukumomin alhazai na jihohi da su gaggauta maida kuɗaɗen ajiya da maniyyata su ka biya domin tabbatar da gaskiya a wajen shirye-shirye na aikin Hajjin bana.