Hajjin 2022: Ba mu fara karɓar kuɗaɗen Hajji ba – Hukumar Alhazai ta Kano

0
394
KANO FIRTS FLIGHT

Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta ce ba ta fara karɓar sabbin kuɗaɗen ajiya na aikin Hajjin 2022 ba a halin yanzu.

Shugaban Hukumar, Abba Muhammad Dambatta ne ya baiyana haka a taron manema labarai a jiya Talata.

Ya ce har yanzu hukumar ba ta buɗe kofar karɓar kuɗaɗen ajiya da ga maniyyata aikin Hajjin bana ba.

Dambatta, wanda ya tabbatar da cewa hukumar za ta dawo da shirin bita ga maniyyata, ya baiyana cewa za su baiwa wanda ya fara biyan kuɗi ne kulawa.

“Duk da cewa mu na ci gaba da jiran adadin kujerun da za a bamu da ga NAHCON, za mu fi baiwa wadanda su ka bar kuɗin su a wajen mu basu karba ba shekaru biyu da ba a yi aikin Hajji ba.

“Wasu sun karbi kuɗaɗen su , wasu kuma har yanzu ba su karba ba, to su xa mu baiwa kulawa ta musamman, sun kai su wajen 3,000.

“Za mu sanar da ranar da za a fara karbar biyan kuɗaɗe amma sai mun karɓi adadin kujerar da za a baiwa jihar nan da ga NAHCON,” in ji Dambatta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here