Kamishiniya a NAHCON ta hori Hukumar Alhazai ta Naija kan yin aiki mai nagarta

0
310

Kwamishiniyar Tarayya, mai wakiltar Arewa ta Tsakiya a Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Hajiya Halima Jibril, ta yi kira ga Hukumar Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Naija da ta tabbatar da bada kulawar da ta dace ga maniyyatan jihar, musamman a ɓangarorin Adashin gata na Hajji, wato Hajj Savings Scheme, ilimantar da maniyyata da kuma hidima gare su.

Hajiya Halima ta yi wannan kira ne yayin wata ziyarar aiki da ta kai wa hukumar a jiya Talata a Minna.

Kwamishiniyar ta bayyana dalilin ziyarar ta ta na cewa ta zo ne domin ganawa da shugabannin hukumar dan tattauna wa yadda za a ɓullo wa shirye-shiryen aikin Hajjin 2022.

Da ya ke jawabi yayin ziyarar, Sakataren Hukumar Hajji na Jihar NIja, Alhaji Umar Makun Lapai, ya taya murna ga Hajiya Halima Jibril, tare da ba ta tabbacin a shirye suke su yi aiki bilhaƙƙi wajen yi wa maniyyata hidima yadda ya kamata.

Ya ci gaba da cewa, duk da dai hukumar ta samar da zarafin adashin gata don tanadin kuɗin zuwa Hajji amma har yanzu babu ko mutum guda da ya nuna buƙatarsa kan haka.

Haka nan, ya taɓo batun maniyyatan da ke kan turba tun daga lokutan baya yana mai cewa, su ne ya kamata a soma kulawa da su yayin shirin Hajjin 2022.

Daga nan, ya buƙaci Kwamishiniyar da ta taimaka ta shawarci NAHCON dangane da batun yin rijistar maniyyatan da ba su karɓi kuɗaɗen su na ajiya ba don cika wa maniyyatan alƙawarin da aka yi musu a lokutan Hajjin 2020/2021 da ba a samu gudanarwa ba sakamakon annobar korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here