Ummara: Saudiya ta soke wajibcin yin allurar korona kafin shiga masallatan Harami

0
445

Hukumar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta canja wasu sharuɗɗa da ta gindaya wa alhazan gida da na ƙasashen waje domin yin Ummara.

Da ga cikin sharuɗɗan, Hukumar ta soke wajibcin nuna sakamakon yin allurar korona ta manhajar Tawakkalana kafin alhaji ya shiga cikin Masallatan Harami Guda Biyu.

Hakan na nufin kafin alhaji ya shiga ƙasar Saudiya dole zai nuna shedar ya yi allurar korona karo na ɗaya da na biyu.

Sai dai kuma ƙasar ta soke nuna shaidar a yin rigakafin a matsayin mataki na shiga masallata Haramin Makka da Madina.

Haka zalika kasar ta soke nuna shaidar yin rigakafin kafin maniyyaci ya samu izinin yin Ummara kamar yadda tsarin ya ke a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here