Hajjin bana zai yi jama’a, in ji Saudiyya

0
418

Hukumomi a Saudiyya sun ce dubun dubatar alhazai na gida da na ƙasashen waje ne za su gudanar da aikin Hajji na bana, saɓanin adadi ƙalilan da suka yi aikin na 2020 da 2021.

Kafar yaɗa labarai ta Haramain Sharifain ta ambato mai magana da yawun ma’aikatar aikin Hajji yana cewa “Hajjin bana zai kasance na adadi mai yawa”.

Ci gaban na zuwa ne kwanaki ƙalilan da Saudiyya ta cire dukkan dokokin kariya daga kamuwa da cutar korona, ciki har da ɗage wajabcin saka takunkumi a bainar jama’a.

Mutum 60,000 ne kacal su ka gudanar da ibadar a shekarar 2021, yayin da ba su wuce 1,000 ba a 2020 sakamakon annobar korona da ta nakasa harkoki a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here