Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, Lawal Abdullahi ya nemi haɗin kan Hukumar Kare Fararen Hula, Civil Defence domin tabbatar da nasarar jigilar aikin Hajjin bana.
Shugaban ya nemi haɗin gwiwar ne yayin da ya karɓi Kwamandan Civil Defence na jihar, Athanasious Sparks da muƙarraban sa da su ka kai masa ziyara a ofishin sa a Gusau a jiya Juma’a.
Ya ce ziyarar ta zo daidai lokacin da za a fara jigilar alhazai na Hajjin bana.
Tun da fari, a nasa jawabin, Kwamandan ɗin ya ce ya fara ziyarar aiki ne domin shida wa hukumar alhazan ƙudurin su na bada gudunmawa a jigilar aikin Hajjin bana.
Ya ce haɗin gwiwa tsakanin hukumar alhazan da Civil Defence na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa tsaro a yayin jigilar aikin Hajji.
Kwamnadan ya yi alƙawarin kawo jami’an sa wadanda za su yi aiki tare da ma’aikatan hukumar alhazan kafin, lokacin da kuma bayan jigilar aikin Hajjin bana.