Hajji 2022: Shugaban NAHCON ya kai ziyara Saudiya domin sanin yadda tsare-tsaren kamfanin Mutawif ya ke

0
273

Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON Barrister Zikrullah Kunle Hassan ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar Saudiyya domin sanin sabon tsarin gudanar da kamfanin Mutawif na Alhazai daga kasashen Afrika da ba na Larabawa wanda aka fi sani da Mu’assasa.

Ziyarar ta biyo bayan bukatar hakan domin sanar da shugabannin NAHCON da sabon tsarin da aka kafa na matsayin kafa wanda gwamnatin Saudiyya ta canza masa zuwa kamfani don inganta ayyuka.

Ana fatan hukumar ta NAHCON za ta yi cikakken bayani a kan sabuwar rawar da hukumar za ta taka wajen gudanar da aikin Hajji.

Hakazalika daga cikin jigon ziyarar akwai alfarmar yin bincike tun farko kan sabbin tsare-tsare na aikin Hajji mai zuwa 2022.

Tawagar Najeriya ta samu tarba daga Mataimakin Shugaban Kamfanin, Mista Muhammad Burhan Saifuddeen a hedkwatar Kamfanin da ke Makkah. in Jeddah, Amb. Abdulkareem Mansur.

Daga cikin tawagar shugaban akwai jami’in hulda da jama’a na NAHCON a Makkah, Uztaz Lamim Abubakar, da mataimakinsa na musamman (Technical) Dr Danbaba Haruna da kuma na musamman mataimakinsa, Alhaji Bunyamin Omowabi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here