Hajji 2022: Gwamnatin Legas ta yi alƙawarin yi wa maniyyatan jihar hidima ingantacciya

0
343

Gwamnatin Jihar Legas ta yi tabbatar wa da maniyyatan jihar cewa za ta yi musu hidima ingantacciya yayin aikin Hajjin 2022.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa ta yini-uku da Hukumar Alhazai ta Jihar Legas da kuma maniyyatan jihar sakamakon janye duk wasu sharuɗɗa na korona da Saudi Arebiya ta yi, wanda ya gudana a Masallacin Shamsi Adisa Thomas (SAT) da ke tsohuwar Sakateriya a GRA, Ikeja.

Sanwo-Olu, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Anofiu Olanrewaju Elegushi ya yabawa maniyyatan a bisa juriya da hakuri da su ka yi lokacin da a ka dakatar da zuwa aikin hajji.

Ya kuma yaba musu a bisa yarda da amince wa da su ka yi ga Hukumar alhazan jihar da su ka bar kuɗaɗen kujerar Hajji da su ka biya a hannun Hukumar.

Gwamnan ya tabbatar wa da maniyyatan cewa aljazan jihar za su samu ingantacciyar hidima a ƙasar Saudiya tun da ga zuwan su har dawowar su gida Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here