Za a caji Riyal 25,000 a matsayin tara ga duk wani kamfanin jigilar Ummara da ya bari alhajin sa ya ƙara kwanaki bayan bizar sa ta ƙare.
Ofishin hada-hadar fasfo na Saudi Arebiya, wanda da larabci a ke kira Jawazat ne ya sanar da hakan.
Kaftin Abdul Rahman Al-Qathami, ya ce kamfanunuwan jigilar Hajji da za a ci tarar sabo da su ne da alhakin mayar da alhazai ƙasashen su kafin wa’adin bizar su ya ƙare.
A cewar Al-Qathami, kamfanunuwan jigilar Hajji da Ummara na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen tabbatar da bin ƙa’idoji da dokokin biza, musamman duba da cewa yanzu an dawo da zuwan alhaxai da yawa.
Ya baiyana cewa tun a baya an gayyaci wakilan kamfanunuwan domin binciken zargin karya dokokin biza da a ke yi musu.
Ya ƙara da cewa a hakan sai da a ka kama kamfanunuwa 208 da kaifin karya dokokin biza kuma an hukunta su ta hanyar cin su tara, inda ya ce tarar ta na farawa ne da ga Riyal 25,000 a kan kowanne Alhaji da ya ƙara kwanaki bayan ƙwarewar wa’adin bizar sa.