Hukumar alhazai ta Adamawa ta samar da kamfanin jigilar Hajji da Ummara

0
406

Hukumar jin daɗi da walwalar alhazai ta Jihar Adamawa ta sanar da samar da wani kamfani da zai riƙa jigilar Hajji da Ummara, mai suna Adamawa Hajj and Umrah Tour Company Limited.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar, a ranar Litinin ne kamfanin ya yi taron faraktoci Kano na farko.

Sanarwar ta baiyana cewa shugaban hukumar alhazai ta Adamawa, ImamBappari Umar Kem shine shugaban kamfanin, inda Babban Sakataren hukumar, Mallam Salihu Abubakar, shine Manajan-Darakta na kamfanin.

A jawabinsa, Salihu Abubakar ya ce kamfanin na kasuwanci ne da zai riƙa yin jigilar Hajji da Ummara a kowacce jiha a fadin kasar nan.

Ya kuma yaba wa Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri bisa sahalewa da ya bayar ta a buɗe kamfanin.

Ya kuma nemi haɗin kai da goyon bayan daraktocin wajen tafiyar da kamfanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here