Saudi Arebiya ta ƙaddamar da wata manhaja ta neman bizar Hajji da Ummara ta wayar salula a Birtaniya.
Saudiya ce ƙasa ta farko a duniya da ta ƙirƙiro da hanyar yin rijistar biza ta wayar salula.
Sabuwar manhajar za ta baiwa maniyyaci dama ya shigar da duk bayanansa da hotuna, ya kuma ajiye sau kafin ya je ofishin buga bizar domin karɓo wa.
Sai dai kuma dole ne bayanan da maniyyaci ya bayar a manhajar ya kasance ya yi daidai da wanda zai kai ofishin buga bizar.
An kirkiro da wannan sabuwar hanyar domin saukaka hanyoyin kula da boda a Birtaniya.
Tun a bara ne dai Ministan Harkokin Waje na Saudiya, Faisal bin Farhan ya ƙaddamar da manhajar bisa umarnin Yarima Muhammad Bin Salman.
Manhajar kuma ta samu ne da haɗin gwiwar hukumomi da dama na harkokin Hajji da Ummara a Saudiya.