Babban Ofishin kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya raba na’urar jin magana 200 ga mata da ba larabawa ba domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Masallatan Haramin guda biyu.
Shafin Haramain Sharifain ya wallafa cewa an ɗauki matakin ne domin baiwa mata da ba larabawa ba damar sauraron huɗubar sallar Juma’a da fahimtar ta.