Hajj 2022: Kano ta fara shirye-shiryen mayar da kuɗaɗen Alhazai kan tsarin adashin gata

0
446
KANO FIRTS FLIGHT

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta fara shirye-shiryen mayar da kuɗaɗen ajiya da maniyyata su ka biya na Hajji kan tsarin Adashin Gata na Hajji, HSS, a shirye-shiryen ta na aikin Hajjin 2022.

Tuni dai hukumar alhazai ta Kano ta sanya takunkumin hana biyan kudaden ajiya na hajji (ta banki ko tsabar kudi), na wannan shekarar har zuwa wani lokaci.

Babban Sakataren hukumar, Alh. Muhammad Abba Danbatta wanda ya bayyana haka a jiya a lokacin da ya ke duba aikin shigar da bayanai da ake ci gaba da yi, hakan ya zo ne bisa bin umarnin Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON.

Alh. Muhammad ya bayyana cewa shirin shigar da bayanan na kafin a mayar da kuɗaɗen kan tsarin HSS a hukumance zai baiwa hukumar damar sabunta bayanai da sauran bayanan da suka dace na mahajjatan Kano.

Sakataren, wanda ya tunatar da cewa mayar da kuɗaɗen maniyyata zuwa HSS ya dogara ne akan kashi 60 cikin 100 a kan HSS da kuma kashi 40 cikin 100 na tsarin “biya na cikin kuɗin ” ya jaddada cewa Kano na daukar sabon tsarin aikin hajji.

Alh. Muhammad ya ce har yanzu hukumar tana dakon sanarwar NAHCON dangane da kason kujerun Hajji da za a baiwa Kano da kuma adadin kudin aikin hajjin bana, ya kara da cewa za a yi la’akari da “first come first service”.

Ya kara da cewa jihar Kano tana da maniyyata kusan 3,000 wadanda suka bar ajiya na shekarar 2020/2021 a hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here