Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan, ya jagoranci tawoga zuwa ofishin jakadancin Saudiya a Nijeriya domin kammala shirye-shiryen biyan diyya ga wadanda haɗarin faduwar ƙarafen ginin Masallacin Harami na Makkah ya shafa.
Tawogar ta haɗa da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi, lauyoyi da ke wakiltar iyalan wadanda abin ya shafa sai kuma Ambasada Bolaji Akinremi, Daraktan Jakadanci da Aiyukan Shari’a.
Da ya ke jawabi a yayin ziyarar, Hassan ya yaba wa gudunmawar ofishin jakadancin Saudiya a Nijeriya da na Nijeriya a Saudiya wajen tsara yadda biyan diyyar zai kasance.
Ya kuma yaba wa shugabannin kasashen biyu a bisa goyon bayan da su ka baiwa jami’an da a ka ɗora wa nauyin aikin rabon, kuma a ka gudanar da shi cikin nasara
Da ya ke jawabi yayin damƙa diyyar ga gwamnatin Nijeriya, Ambasadan Saudiya a Nijeriya, Faisal Bn Ibrahim Al-Ghamidy, ya karrama sahihan waɗanda za su amfana da diyyar a gaban Shugaban NAHCON, Hassan.
Ya yi kira ga ƴan uwan wadanda abin ya shafa da su ji tsoron Allah wajen baiwa iyalan wadanda su ka rasu a haɗarin, inda ya shawarci wadanda su ka samu raunuka da su bi hanya ta daidai su yi amfani da kuɗaɗen.
Al-Ghamidy ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Ma’aikatar Harkokin Waje, NAHCON da kuma lauyoyi wakilan iyalan wadanda abin ya shafa a bisa tsara yadda rabon diyyar ya kasance.
Ya kuma yaba wa Sarki Abdul’aziz Bin Salman a bisa karancin da ya yi wa wadanda haɗarin ya rutsa da su