Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta yabawa Hukumar Alhazai ta Jihar Sokoto bisa jajircewar da ta yi na samar da jin dadi da walwalar alhazai tsawon shekaru.
Daraktan Sa ido da Bin ka’ida na NAHCON, Alhaji Usman Aliyu Shamaki ne ya yi wannan yabon yayin da ya kai ziyarar duba wuraren jigilar Alhazai yayin da a ke tunkarar gudanar da aikin Hajjin 2022.
Alhaji Shamaki ya bayyana jin dadinsa kan abubuwan da ya gani a kasa, inda ya yabawa babban sakataren hukumar Alhaji Shehu Mohammed Dange bisa jajircewarsa na ciyar da hukumar gaba.
A nasa bangaren Alh. Shehu Mohammed Dange ya bayyana cewa ko shakka babu ziyarar za ta karfafa gwiwar ma’aikatan wajen kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu.
Daga cikin tawagar NAHCON akwai Umar M. Kalgo na Outreach Center Abuja, Garba Yakubu Coordinator na shiyyar Sokoto, Kebbi, da Zamfara da Nabila Umar na sashin bayar da lasisi na hukumar.
Daraktan Kudi & Supply Alh Shehu Usman Yahaya, Daraktan Gudanarwa Alh Ibrahim Muhammad Babangida da sauran hukumomi da ma’aikatan hukumar sun samu halarta.