Ramadan: Saudiyya za ta ciyar da mutane miliyan 1.2 a ƙasashe 34

0
472

Saudi Arebiya za ta ƙaddamar da shirin buɗe-baki a ƙasashe 34, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito a ranar Lahadi.

Manufar shirin ita ce samar da abincin buɗe-baki ga Musulmi a cikin watan Ramadan, wanda ake fatan soma wa a ranar 2 ga watan Afrilu.

Ana sa ran mutane miliyan 1.2 za su ci gajiyar shirin.

Rahotannin sun ce Ma’aikatar kula da Harkokin Addinin Musulunci, ta kammala dukkanin shirye-shiryen da suka wajaba domin ganin shirin ya shafi ɓangarorin duniya, ko da yake ya dogara daga neman buƙatar hakan da ga ƙasashen.

Za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar ofisoshin jakadancin Saudiyya da cibiyoyin addinin Musulunci na ma’aikatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here