Gwamnatin Najeriya ta amince da kafa Cibiyar Horas da Aikin Hajji

0
506

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta amince da kafa Cibiyar Horas da Aikin Hajji ta Nijeriya, HIN, da nufin bunƙasa ma’aikata a fannin aikin Hajji da Ummara a ƙasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAH|CON, Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce an bayyana amincewa da kafa cibiyar ne a ranar Talata a yayin taronn farko na Kwamitin gudanarwa da Masu ruwa da tsaki kan Tsare-tsare mai inganci na Hukumar a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa tun a ranar 22 ga Afrilu, 2016, karkashin jagorancin Abdullahi Mukhtar-Muhammad tsohon shugaban NAHCON, ka fara saka ɗambar kafa cibiyar.

A cewar sanarwar, Mukhtar ya kaddamar da kwamitin kafa cibiyar horarwas, karkashin jagorancin Farfesa Abubakar A. Mustapha, da kuma Dokta Saleh Okenwa a matsayin shugaba tare da wasu mambobi 12 da suka hada da shugaban hukumar NAHCON na yanzu. , Zikrullah Kunle-Hassan.

Sanarwar ta ce: “Wannan kwamitin yana da manufofi biyar ne kuma an mika rahotonsu ga Shugaban Hukumar NAHCON na lokacin a ranar Laraba 5 ga watan Yuni, 2016.

“Bayan tattaunawa da masana daban-daban, shawarwari, samo ƙwararrun da za su yi aikin, a karshe dai kwamitin gudanarwa na NAHCON ya kafa kwamitin ba da shawara kan fasaha don taimakawa hukumar wajen ganin an kafa cibiyar aikin Hajji.

“An kaddamar da kwamitin kuma ya fara aiki a watan Satumba, 2020.

“Bayan haka, a ranar Talata 19 ga watan Agusta, 2020, Shugaban Hukumar NAHCON ya mika wa babban sakataren hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) takardar neman amincewar kafa Cibiyar Hajji ta Najeriya,” in ji Usara.

Ta kara da cewa haka NAHCON ta yi ta faɗi-tashi har zuwa lokacin da a ka amince da kafa cibiyar.

Shugaban NAHCON Barista Kunle Hassan, ya bayyana nasarar da aka samu a matsayin wani abin farin ciki na kashin kansa, kasancewar sa cikin tawagar a lokacin da ake gudanar da aikin.

Ya kuma yi godiya ga Ubangiji da ya ba wa hukumar damar kai wa ga wannan mataki na kafa HIN.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here