An yi wa Haramin Makka ado da darduman sallah na alfarma guda 25,000

0
309

An yi wa harabar Masallacin Harami na Makka ado da dardumai na alfarma guda 25,000 domin baiwa masallata damar yin ibada cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Hukumar kula da Harabar Masallacin ta ce hakan na ɗaya da ga cikin matakan da ta ɗauka na tsaftace Masallacin kamar yadda hukumomin ƙasar su ka bada umarni, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta SPA ta rawaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here