Hajjin 2022: Jabal al-Rahma zai sha kwalliya

0
357

Saudi Arebiya ta ƙaddamar da wani aiki na ƙawata guraren da ke jikin dutsen Rahama, wanda a ka fi sani da Jabal al-Rahma.

A aikin ƙawatawar, za a saka fitilu a kan dutsen da kuma harabar sa.

Hakazalika, za a ƙawata yankin da na’urorin canjin yanayi da na feshin ruwa, gami da shimfiɗa korayen ciyayi a filayen yankin domin masu tafiya a ƙafa, kantuna, ɗakunan cin abinci da na shan shayi, inda za a kuma a samar da guraren da za a kunna telebijin domin kallo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here