A karo farko, an buɗe sabbin zaurukan sallah tamanin da ke cikin kashi na uku na aikin faɗaɗa masallacin Harami na Makkah ga masallata a cikin watan Ramadan na wannan shekara, kamar yadda Babban Ofishin kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya sanar.
Walid Al-Masoudi, Babban Daraktan Gudanarwa na aikin fadada masallacin Harami zango na uku, ya ce sabbin zaurukan na nan ne a kasa da kuma hawa na daya da na biyu na masallacin.
Masu ibada na iya shigar su ta kofofin shiga da dama a bangaren arewa, yamma da gabas na masallacin, da kuma babbar kofar shiga, in ji shi.
Sabbin zaurukan da a ka samar za su rika ɗaukar kashi 95 cikin 100 na yawan zaurukan yin sallah a cikin sashen masallacin da ke dauke da su, wanda a yanzu za su iya daukar masallata har 300,000. Idan waɗannan ɗakunan ciki sun cika, farfajiyar arewa za ta iya ɗaukar ƙarin masu ibada 280,000 kuma akwai sarari na ma fiye da haka a farfajiyar yamma.
Al-Masoudi ya ce adadin masu ibada a masallacin yana karuwa a cikin watan Ramadan kuma akwai tawaga da za su tabbatar da cewa za su iya zagayawa, gano sabbin wuraren sallah da shiga da fita cikin sauki da aminci.
Ya kara da cewa, ana gudanar da dukkan ayyukan ne a karkashin kulawar Mohammed Al-Jabri, karamin sakataren aiyuka da fage da kuma kare muhalli a fadar shugaban kasa, karkashin jagorancin shugabanta Sheikh Abdulrahman Al-Sudais. daidai da manufofin shugabancin Masarautar na samar da ingantattun ayyuka ga maziyartan Masallatan Harami guda biyu.
Za a iya shiga sabbin zaurukan sallar ta babbar kofar masallacin, kofar sarki Abdullah mai lamba. 100, tare da kofofi 104, 106, 112, 173, 175, da 176 a bangaren arewa, kofofi 114, 116, 119, 121, da 123 a bangaren yamma, kofofi 162, 165 da 169 a bangaren gabas.