Majalisar Wakilai ta yanke hukuncin baiwa Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON umarnin dakatar da shirin Adashin Gata na Hajji, wanda a ka fi sani da Hajj Savings Scheme, HSS.
Wannan yazo ne bisa wani ƙuduri da ɗan majalisa daga Jihar Katsina, Aminu Ashiru Mani ya miƙa, kan buƙatar a gaggauta bincikar shirin.
Dan majalisar ya ce an ƙirƙiro da shirin ne a 2006 domin maniyyata su samu damar yin adashin gata don zuwa aikin Hajji.
Mani ya ƙara da cewa, a cikin shekaru 2 na ƙaddamar da shirin, bisa haɗin gwiwa da bankin Jaiz domin taimaka wa maniyyata su tara kuɗin zuwa aikin Hajji, yawan kwastomomin bankin ya karu da 4,000 inda kuma tuni a ka tara Naira Biliyan 1.
Ya nuna damuwa kan zargin rashin gaskiya da amana a shirin na HSS.
“Idan a ka bar wannan haka, to zai haifar da badaƙalar kuɗaɗe a tsarin da kuma rashin bin doka,”
A nashi ɓangaren, Mataimakin Kakakin Majalisar, Ahmed Wase ya yi bayanin cewa shekaru biyu kenan maniyyata na zuba kuɗi a asusun adashin gatan amma ba su samu zuwa aikin Hajjin ba sabo da korona.
Wase ya zargi NAHCON da karya doka da duma hannu a cikin kuɗaɗen.
Da ga bisani sai a ka umarci kwamitin harkokin alhazai domin ya gudanar da bincike a kan shirin Adashin Gata na Hajji.
Hakazalika majalisar ta umarci kwamitin da ya sake yin nazari a kan ɗaukacin yarjejeniyar da NAHCON ta kulla da Jaiz , sannan ya mika wa majalisar rahoto a cikin makonni biyu.