Dakatar da Adashin Gata na Hajji: NAHCON ta mayar wa da Majalisar Wakilai martani

0
397

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta musanta zarge-zargen da Majalisar Wakilai ta yi mata a kan shirin Adashin Gata na Hajji, HSS, inda ta yi zargin a na yin cuwa-cuwa a tsarin.

A jiya Alhamis ne dai Majalisar Wakilai a wani ƙuduri da ɗan majalisa daga Jihar Katsina, Aminu Ashiru Mani ya miƙa, ta bada umarnin a gaggauta bincikar shirin HSS.

Dan majalisar ya ce an ƙirƙiro da shirin ne a 2006 domin maniyyata su samu damar yin adashin gata don zuwa aikin Hajji.

Sai dai kuma a wata sanarwa da ta zamto martani ga majalisar, mai ɗauke da sa hannun Mataimakiyar Daraktan Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Usara, hukumar ta ce a ranar 4 ga watan Oktoba, 2020 a ka ƙaddamar da shirin ba wai a 2006 kamar yadda majalisar ta faɗa ba.

NAHCON ta ƙara da cewa, a batun almundahanar da Majalisar ke zargi, ko wanne mutum da ya yi rijista da shirin yana karɓar bayanin asusun duk karshen wata ta wayar salula har da ma robar da s ke samu, inda ta ƙara da cewa maniyyata da ke kan tsarin ka iya duba asusun su ta wayar su a duk lokacin da su ke bukata.

Hakazalika a sanarwar, hukumar ta fitar da jadawalin rabon robar da s ka samu a Adashin Gata na Hajji ɗin na ko wacce jiha da ga sanda a ka ƙaddamar da shi zuwa watan Disamba 2021.

NAHCON ta kuma musanta batun kasar kuɗin da s ke tara wa a shirin, inda ta ce kuɗin da a ka tara, wanda ya kai N 3,583, 243,940.00, an a ajiye su a asusun Babban Bankin Nijeriya, CBN har zuwa farkon shekarar nan da a ka mai da su asusun ko wacce jiha da ke cikin shirin.

A ƙarshe, NAHCON ta nemi da a turo Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa, EFCC da tazo ta binciki yadda s ke tafiyar da Adashin Gata na Hajji ɗin sannan ya binciki yadda s ke tafiyar da kuɗaɗen a Hukumomin Alhazai na Jihohi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here