Saudi Arebiya ta baiyana cewa maniyyata 850,000 ne, daidai da kashi 85 cikin 100, za su yi aikin Hajjin bana daga cikin mutum miliyan 1 da ƙasar ta ce za su yi ibadar ta bana.
Tashar Al-Arabiya ta rawaito cewa wasu sahihan majiyoyi makusanta sun baiyana cewa alhazan cikin ƙasar 150,000 ne kawai za su yi aikin Hajjin na bana, daidai da kashi 15 cikin ɗari.
Majiyoyin sun ce hikimar hakan ta zo ne duba da yadda alhazan ƙasashen wajen Saudiya ɗin ba su samu damar yin aikin Hajji ba a shekarun 2020 da 2021 ba sakamakon annobar korona.