Ramadan: Alhazan Ummara miliyan 2 sun samu ingantacciyar hidima a kwanaki goman farko — Sudais

0
313

Sheikh Abdulrahman Al-Sudais, Shugaban Babban Ofishin kula da Harkokin Masallatan Harami guda biyu, ya bayyana cewar ofishin nasa ya samu nasarar bayar da ingantacciyar hidima ga alhazan Ummara sama da miliyan biyu na a cikin kwanaki goman farkon na watan Ramadan.

Ofishin ya samu nasarar kammala alhazan sama da miliyan biyu a rukuni-rukuni cikin kwanciyar hankali sakamakon kokarin da ya ke yi da hada kai da wasu ƙwararru na musamman.

“Wannan ƙoƙarin ya haifar da samar da mafi kyawun ayyuka ga alhazai kuma hakan ya taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu cikin sauƙi da jin daɗi a cikin yanayi na na ibada tare da tsaro,” in ji shi.

Sheikh Al-Sudais ya ce Masallatan Harami guda biyu sun sami kwararar mahajjata da maziyarta da masu ibada a cikin kwanaki 10 na farkon watan Ramadan bayan da aka sassauta mafi yawan matakan kariya da ka’idojin kariya daga kamuwa da cutar korona.

Shugaban ya kara da cewa, tare da hadin gwiwar sauran hukumomi, sun himmantu wajen samar da ingantattun hidimomin hadaka ga mahajjata da masu ibada, wanda hakan ya yi daidai da matakan kiyaye lafiya don tabbatar da tsaron lafiyar alhazai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here