‘Allah ya zaɓe ni’: Shahararren mawakin kasar Koriya ta Kudu ya yi aikin Ummara bayan ya Musulunta

0
330

Shauƙi ya tashi sosai lokacin da fitaccen mawaƙin nan na ƙasar Koriya ta Kudu, Daud Kim ya isa Makka domin gudanar da aikin Ummara.

A shekarar 2020, Daud, wanda aka fi sani da Jay Kim, ya bayar da sanarwar ba zata a dandalinshi na sada zumunta cewa ya yanke shawarar shiga addinin Musulunci.

Da ga baya ya canza sunansa daga Jay zuwa Daud.

Bayan annobar korona, sai ya yanke shawarar shiga aikin Ummara, inda ya shiga shafinsa na Instagram ya riƙa saka hotuna da kuma wallafa saƙuna daban-daban.

Daga nan ne Dauda ya saka jerin hotunansa a Masallacin Harami a dakin Ka’aba da faifan bidiyo na kewayen masallacin.

“A karshe na zo Makka. Nine nafi kowa sa’a domin Allah SWT ya zabe ni ya kawo ni. Masha Allah,” ya wallafa a shafinsa.

Yace ya yi addu’a ga daukacin al’ummar musulmi na duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here