An samu aukuwar gobara a sansanin alhazai na Kano inda wuta ta lakume sahguna hudu tare da lalata kaya na milyoyin Naira.
Rahotanni sun baiyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe bakwai na yammacin Juma’a, tare da lalata shagunan da galibi ake sayar da tufafin Larabawa.
Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar da lamarin ya shafa, Hajiya Aisha Abduljalal, ta ce an kira ta tare da shaida mata cewa gobarar ta tashi a kantin ta, inda ta ƙara da cewa, ko da ta isa wurin sai ta tarar da shagonta na ci da wuta kuma babu wani abu da ya rage a shagon.
Da yake yi wa manema labarai karin haske kan ibtila’in, shugaban kasuwar, Alhaji Auwalu Ahmad Shinkafi, ya ce ba su kai ga tantance adadin hasarar da aka tafka a gobarar ba.
Ya kara da cewa, “Musabbabin gobarar ba ya rasa nasaba da matsalar lantarki. Kuma ba mu san iya hasarar da gobarar ta haifar ba, sai dai miliyoyin Naira ake magana, za mu sanar da ku idan muka samu takamammen adadin hasarar da aka yi.
“Mun kira jami’an kwana-kwana da sauran hukumomi da lamarin ya shafa inda suka ba mu hadin kai wajen kashe gobarar.”
Sa”ilin da yake tabbatar da aukuwar gobarar, mai magana da yawun Hukumar Kwana-kwana ta Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce jami’ansu sun hallara waurin gobarar a kan lokaci kuma sun samu nasarar kashe gobarar.