YANZU-YANZU: NAHCON ta bada kujerun Hajji 33,976 ga hukumomin alhazai na jihohi

0
731

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta baiwa hukumomin alhazai na jihohi 36 da Abuja kason kujerun Hajji 33,976.

A jiya Laraba ne dai NAHCON ɗin ta sanar da cewa Saudi Arebiya ta bata kason kujerun Hajjin bana 43,008.

Sai dai kuma a yau Alhamis, hukumar ta sanar da cewa ta baiwa jihohi 36 na ƙasar nan kason su na kujerun Hajji har 33,976.

Sannan kuma NAHCON ta baiyana cewa ta baiwa kamfanonin jigilar aljazai masu zaman kansu adadin kujeru 9,032 na Hajjin 2022.

A tuna cewa a makon da ya gabata ne dai Saudiya ta sanar da cewa aljazai miliyan ɗaya ne, na gida da na waje za su yi aikin Hajjin bana.

Kasar ta ce alhazai da ga ƙasashen waje 850,000, sai kuma alhazan cikin ƙasar, 150,000 ne za su yi aikin Hajjin na 2022.

Shekaru biyu kenan rabon da Saudiya ta bar alhazai daga wajen ƙasar su yi aikin Hajji sakamakon annobar COVID-19, wacce a ka fi sani da korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here