Farashin aikin Hajji ya tashi da kashi 40 a Kuwait

0
430

Wata jaridar cikin gida ta yi hasashe cewa farashin tafiye-tafiyen aikin Hajji da ga Kuwaiti don sauke farali a kasar Saudiyya zai karu da kashi 40 cikin 100 a bana, bayan an rage kason da aka ware wa ƙasar.

Saudiyya ta rage wa Kuwait adadin alhazai daga 8,000 kafin annobar korona zuwa 3,622 Hajjin bana, Sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewa a na ta kokarin rage farashin tafiye-tafiyen na aikin Hajji a bana a ƙasar.

Jaridar ta ce farashin jigilar Hajji daga Kuwait a bana ana sa ran zai tashi daga KD3,000 zuwa KD4,000, wanda ya karu da kusan kashi 40 cikin 100 idan aka kwatanta da lokutan baya.

Wata majiya da ba a tantance ba ta ce mahukuntan Kuwaiti za su ware kashi 15 cikin 100 na alhazan kasar ga tafiye-tafiyen Hajji mai saukin farashi, sannan za su sa ido sosai da su don tabbatar da bin ayyukan da aka ayyana da kuma wajabta masu gudanar da shirye-shiryen dawo da kudaden hidimomin da ba a yi wa alhazai su ba.

Shawarwari da aka yi don shawo kan farashin Hajji, a cewar takardar, sun hada da zabar masu shirya alhazan da ke ba da farashi da ayyukan da suka dace; ba da tallafin irin waɗannan kamfen; soke ayyukan da ba su da mahimmanci yayin aikin hajji; da yin yunƙurin ƙara kason tafiye-tafiyen Hajji mai rahusa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here