Hukumar Alhazai ta Jihar Naija ta ce wajibi ne kowanne maniyyacin Hajjin bana a jihar ya tabbatar da ya yi rigakafin cutar korona.
Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar, Alhaji Umar Makun Lapai ne ya yi wannan bayanin a lokacin da ya ke yi wa jami’an kula da ofisoshin Hajji na shiyyoyin jihar (APWOs) bayanin sakamakon ganawarsu da NAHCON da suka yi kwanan nan a Abuja.
Makun Lapai ya ce sharaɗi ne ya kasance maniyyatan jihar sun yi rigakafin korona na ɗaya da na biyu hada da allurar ‘booster jab’.
Ya ci gaba da cewa, babban dalilin ganawarsu da jami’an shi ne don sanar da su adadin kujerun Hajji da jihar ta samu da kuma abin da kananan hukumomin jihar za su samu.
Daga nan, ya nusar da jami’an kan su shaida wa maniyyatan yankunansu da su tanadi kudin ciko saboda akwai yiwuwar daga farashin kujerar Hajji zuwa kimanin miliyan N2.5.
Haka nan, ya gargadi jami’an a kan kada su soma karbar kudade daga hannun maniyyatan har sai an samu izini daga wajen uwar hukuma ta kasa (NAHCON). Tare da jaddada musu bukatar da ake akwai a kan su fadakar da maniyyatan muhimmancin kowannensu ya tanadi lambobinsa na BVN da NIN ko da bukatarsu ta taso.
A nasu bangaren, jami’an sun yaba tare da nuna gamsuwarsu kan dukkan bayanan da aka yi musu, suna masu cewa a shirye suke su yi aiki dad a gaskiya.