Maniyyata 1,403 ne ake sa ran za sauke farali a kasa mai tsarki daga Jihar Kwara yayin Hajjin bana.
Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Kwara, Alhaji Abdulganiyi Ahmed ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Litinin a llorin.
Sakataren ya ce, kujerun Hajji 1,403 ne Kwara ta tsira da su daga cikin kujeru 43,000 da aka bai wa Nijeriya. Tare da cewa, an tabbatar wa Kwara da nata kason ne yayin wani taro da aka yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi a Abuja.
Ahmed ya kara da cewa, Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta amince ta kasafta kujerun Hajji 43,000 da ta samu daga Saudiyya a tsakanin jihohin kasa.