Saudiya ta ƙirƙiri abun-hannu mai na’ura domin nemo yaran da su ka ɓata a Harami

0
450

Shugaban Babban Ofishin kula da Masallatan Harami Guda Biyu, Sheikh Dakta Abdulrahman Al-Sudais, ya ƙaddamar da wata na’urar ɗaura wa a hannu mai ɗauke da na’ura mai ƙwaƙwalwa da za a iya gana wa da iyaye cikin gaggawa a Masallacin Harami na Makka.

Kafar yaɗa labarai ta Arab News ta rawaito cewa babban ofishin zai raba na’urar ɗaura wa a hannu ga yara domin nemo su cikin sauki yayin da su ka ɓata a cikin cinkoson jama’a a Harami.

A nashi ɓangaren, Ƙaramin Sakatare-Janar mai kula da jama’a da ayyuka na musamman, Amjad bin Ayed Al-Hazmi, ya ce ofishin kullum na ƙoƙarin ɓullo da hanyoyi ingantattu domin yinwa baƙi hidima s masllatan Harami Guda Biyu.

A hannu guda kuma, ofishin ya raba lema7,000 ga alhazan Ummara da kuma masu ziyarar masallacin Harami na Makka.

A cewar Babban Ofishin, shirin raba lemar, wanda a ka yi wa laƙabi da “Lemar ka a hannun ka”, an ƙirƙiro shi ne domin rage wa alhazan Ummara zafin rana yayin ɗawafi da kuma kare ma’aikata masu yi wa alhazan hidima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here