Hajjin 2022: Gombe ta samu kujeru 1,005 daga NAHCON

0
527

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bads adadin kujerun alhazai 1,005 ga Jihar Gombe domin gudanar da aikin Hajjin 2022.

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Gombe, Alhaji Sa’adu Hassan Adamu ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ganawa da jami’an alhazai na ƙananan hukumomi 11 na jihar, a ɗakin taro na hukumar.

A taron, wanda ya samu halartar da ma’aikatan gudanarwa, Adamu ya kuma sanar da jami’an Alhazan kan ayyuka da shirye-shiryen aikin hajjin bana, inda ya bayyana cewa ana sa ran za a fara bitar alhazai nan take bayan sallah.

Alhaji Adamu ya ƙara da cewa, ana hasashen farashin aikin Hajji zai tashi sabo da halin da tattalin arzikin ya tsinci kansa s yanzu, inda ya kuma shawarci maniyyata da su biya kuɗin ajiya da su tabbatar da cewa kuɗaɗen da su ka ajiye ya kai Naira miliyan biyu da dubu dari biyar (N2,500,000:00) kafin hukumar NAHCON ta bayyana takamaiman kuɗin Hajjin bana a hukumance.

“Kowane mahajjaci dole ne ya dauki kashi na farko da na biyu na rigakafin COVID-19 da kuma Booster jab don samun damar shiga aikin Hajji, kuma za a yi gwajin PCR sa’o’i 72 kafin tashin jirgin kuma mutanen da su ka haura shekaru 65 za su yi aikin Hajji,’ in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here