Hajjin 2022: Bauchi za ta rufe karɓar kuɗin aikin Hajji ran 11 ga Mayu

0
441

Hukumar Jin daɗin Alhazai Musulmai ta Jihar Bauchi ta yi kira ga maniyyata da su ka biya kuɗin ajiya na aikin Hajji da ya kai Naira Miliyan 1.5 ko ƙasa da haka, da su gaggauta cika kuɗin ya kai Naira miliyan 2.5 kafin 11 ga watan Mayu, sannan a jira sanarwar ta gaba daga Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON.

Babban Sakataren Hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris shine yayi kiran a Bauchi yayin wata ganawa da Jami’an Aikin Hajji na Ƙananan Hukumomin, a wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

A wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya fitar, Babban Sakataren ya ce hukumar alhazai ta Bauchi ta samu ƙayyadaddun kujerun Hajji 1,362, inda ya ce za a yi amfani da wanda ya fara zuwa biyan kudinsa ne kawai.

Imam Idris ya ɗora alhakin tashin farashin aikin Hajji da matsalar tattalin arziki da kuma karyewar naira, inda ya ce hakan ne ya sanya a ke ganin kuɗin aikin Hajji zai kai Naira miliyan 2.5 a bana.

Sabo da haka Babban Sakataren ya shawarci maniyyata da su hanzarta cika kuɗaɗen nasu, inda ya ce hakan ne zai baiwa NAHCON damar yin jigilar aikin hajji ta bana cikin sauki.

Ya ce Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya dage wajen cewa an yi wa alhazan jihar ingantacciyar hidima a nan gida Nijeriya da kuma ƙasa mai tsarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here