Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta baiwa Jihar Borno kason ta na kujerun aikin Hajji da su ka kai adadin 1195.
Babban Sakataren Hukumar Alhazai na jihar, Ali Malam Bukar, shine ya bayyana hakan a Maiduguri.
Ya kuma shawarci maniyyata da su ka biya kuɗin ajiya da su ƙara ya kai Naira miliyan 2.5 kafin NAHCON ta sanar da farashin aikin Hajjin na bana.
Bukar ya yi bayanin cewa idan NAHCON ta sanar da farashin aikin Hajjin ƙasa da Naira miliyan 2.5 ɗin, to za a maido wa da maniyyatan sauran kuɗaɗen su.
Ya kuma yi bayanin cewa tashin gwauron zabi da farashin kuɗaɗen ƙasashen Waje ya yi, musamman Dalar Amurka, shi ya haifar da ƙarin farashin aikin Hajji a bana.
Babban Sakataren ya kuma umarci jami’an aikin Hajji na Ƙananan Hukumomin jihar da su wayar wa da maniyyata kai a kan yin allurar rigakafin korona a wani mataki na wajibi kafin yin aikin Hajji.
Ya baiyana cewa a na sauke azumi, ba da daɗewa ba , za a fara yi wa alhazai bita a jihar.