Bizar ziyara ba za ta yi amfani a Hajji ba — Saudiya

0
113

Ma’aikatar Hajji da Ummara ta Ƙasar Saudi Arebiya ta baiyana cewa Musulmai masu riƙe da bizar ziyara zuwa ƙasar ba su da damar amfani da ita wajen yin aikin Hajji.

“Ita bizar Hajji daban ta ke ko kuma ga waɗanda su ke zaune a ƙasar bisa izini” in ji gwamnatin ƙasar, kamar yadda wata jaridar Saudiya Ajel ta rawaito.

Tun a farkon watan nan ne dai Saudiya ta sanar cewa Musulmai miliyan 1 ne za su yi aikin Hajji a ciki da wajen ƙasar nan.

Kasar ta gindaya sharuɗɗan cewa sai Alhaji dan ƙasa da shekara 65, sannan yayi cikakkiyar rigakafin korona da kuma gwajin korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here