Muna nan muna ƙoƙarin rage tashin farashin aikin Hajjin bana — Shugaban NAHCON

0
531
ZIKRULLAH NAHCON CHAIRMAN

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan, ya baiyana cewa hukumar na nan na iya bakin ƙoƙarin ta na ganin cewa an rage farashin aikin Hajji na bana, duk da cewa ba makawa sai an ƙara farashin.

Kunle ya baiyana haka ne a sakon Sallah da ya fitar, wanda ya sanya hannu da kansa a yau Litinin.

A cewar sa, NAHCON na bin hanyoyin da su ka dace don ganin cewa an abu hanyoyin da su ka dace domin ganin cewa ƙarin farashin aikin Hajjin bai yi yawan da har za a koka ba.

Sai dai kuma ya yi kira ga maniyyata da su ma su hanzarta su cika kuɗaɗen su kafin NAHCON ta sanar da farashin aikin Hajji da ta ƙaiyade.

Ya ce biyan kuɗin a kan lokaci zai baiwa hukumar samar sanin adadin alhazan Nijeriya, sai ta yi amfani da hakan wajen yin shirye-shiryen aikin Hajjin.

Hassan ya kuma bayyana sabbin tsare-tsare da a ka ɓullo da su a aikin Hajjin na bana.

Inda ya ƙara da cewa tuni NAHCON ta yi nisa wajen shirye-shirye na aikin Hajjin bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here