Kar ku janyo a hana Nijeriya zuwa aikin Hajji, ƙungiya ta gargaɗi ƴan majalisar taraiya

0
476

Independent Hajj Reporters, IHR, ƙungiya mai zaman kanta wacce ta ke sa ido da kuma kawo rahotanni a kan jigilar aikin Hajji a Nijeriya da Saudiya, ta yi kira ga majalisun tarayya da su dakatar da duk wasu ƙudirori da ka iya janyo a hana Nijeriya zuwa aikin Hajjin bana.

Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a yau Laraba a wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban ta na ƙasa, Ibrahim Muhammad.

A sanarwar, ƙungiyar ta tuna cewa tun da fari, Majalisar Wakilai ce ta fara shigar da kudirin cewa a dakatar da aiwatar da shirin nan na Adashin Gata na Hajji, HSS, inda ita kuma Majalisar Dattawa, ta hannun Sanata Ibrahim Dambaba, mai wakilta Sokoto ta kudu, na neman a canja dokar da ta kafa Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON da ta tilasta wa Hukumar ta maida kuɗin aikin Hajji zuwa a riƙa ajiye shi a asusun Babban Bankin Nijeriya, CBN.

Sai dai kuma IHR ta ce duk da cewa aikin majalisar taraiya na da ikon yi da kuma gyaran doka, amma waɗannan batutuwa da su ka kawo basu kawo su a lokacin da ya dace ba.

A cewar sanarwar, wannan yunkuri na majalisun taraiyar wata gagarumar barazana ce ga makomar aikin Hajji a Nijeriya.

IHR ta yi nuni da cewa alhazai, musamman waɗanda su ke yin rijistar aikin Hajjin 2022, ba su da ruwa da waɗannan ƙudirori na majalisun taraiya.

Ta bada shawarar cewa a kamata ya yi a dakatar duk wani yunkuri na yin kwaskwarima ga dokar da ta kafa NAHCON da aikin Hajji sai bayan an kammala Hajji, in ba haka ba, a cewar IHR, to akwai gagarumar bata zana ta hana Nijeriya zuwa ikon Hajji a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here