Hukumomin Saudiya sun cafke a ƙalla mutane 30 Dlda laifin ɗaga hoton ƴan siyasa a Ka’aba

0
705

Rahotonin daga kasar Saudiyya dai sun yi nuni da cewa hukumomi a ƙasar sun cafke wasu ƴan Najeriya, a ƙalla mutum 30, da ake zarginsu da wuce gona da iri wajen shiga tare da daga hotunan wasu ‘yan siyasa dake neman tsayawa takarar shugabanci a gaban dakin Ka’aba.

Idan za a iya tuna wa, hotunan wasu aljazan Ummara ƴan Nijeriya su ka yi ta yawo a kafafen sadarwa su na ɗauke da fastocin Boka Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar a harabar dakin ka’aba a kwanan nan.

VOA ta tawaito cewa a halin da ake ciki dai majiyar daga Saudiya ta bayyana cewa wadanda aka kama suna hannun mahukunta kasar, karkashin kulawar askarawa domin gurfanar dasu gaban kotu tare da yanke masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata.

Tun dai a cikin watan Ramadana aka yi ta hango yadda wasu ‘yan Najeriya da suka dinga tallar ‘yan siyasar kasarsu a garin makkah, lamarin da hukumomi a kasar suka ce baza su lamunta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here