Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, KSPWB ta ce nan da 12 ga watan Mayu za ta rufe karɓar kuɗin aikin Hajji da ga maniyyata.
Babban Sakataren Hukumar, Mohammad Abba Dambatta ne ya sanar da hakan a yayin ganawa da manema labarai a kan shirye-shiryen hukumar na aikin Hajjin bana a yau Alhamis.
Ya ce za a rufe karɓar kuɗaɗen ne sabo da ana daf da fara jigilar aikin Hajji.
Sabo da haka, Dambatta ya yi kira ga maniyyata da su cika kuɗin da su ka ajiye nan da kwanaki bakwai.
Ya kuma yi bayanin cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta sanya Naira miliyan 2.5 a matsayin kuɗin Hajjin bana sakamakon tashin farashin Dalar Amurka da kuma ƙarin haraji da a ka samu a kasar Saudiya da mlkamfanunuwan sufurin jiragen sama.
Dambatta ya ƙara da cewa kawo yanzu, maniyyata 2,500 su ka bada wani ɓangare na kuɗaɗen aikin Hajjin, inda ya nanata cewa hukumar za ta kula ne da waɗanda su ka ajiye kuɗin su tuntubi a hukumar.