Hajjin 2022: Maniyyata 600 sun kammala biyan kuɗin su a Nassarawa

0
405

Babban Sakataren Hukumar Jin daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Nassarawa, Mallam Idris Ahmad Al-Makura ya baiyana cewa Maniyyata 600 a cikin 684 da Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta baiwa jihar, sun kammala biyan Naira Miliyan 2.5 na kuɗin Hajji.

Ya bayyana haka ne a wata ganawa da jami’an aikin Hajji na Ƙananan Hukumomi a birnin Lafia.

A cewar sa, hukumar ba ta yi wa sabbin maniyyata rijista ba tsawon shekaru biyu, inda ya ƙara da cewa Maniyyata 600 da su ka cika kuɗaɗen su tun waɗanda su ka yi ta ajiyar kuɗaɗen su ne a shekarun da ba a je aikin Hajji ba.

Ya yi kira ga sauran waɗanda ba su cika kuɗaɗen nasu ba da su hanzarta ko sun rasa gurbin zuwa aikin Hajjin bana.

Ya ce hukumar ta kammala shirye-shiryen rufe karɓar kuɗaɗen aikin Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here