Ɗan Pakistan ya tafi aikin Hajjin bana a keke

0
378

Noor Ahmad, ɗan ƙasar Pakistan, ya far bulaguro zuwa yin aikin Hajjin bana a kan keke.

Ahmad ya ɗauki wannan matakin ne domin ya ƙi zuwa Hajjin ta jirgin sama wanda gwamnatin ƙasar ta ke ɗaukar nauyi.

Kamar yadda rahotanni da kafafen yaɗa labarai na ƙasar su ka baiyana, ba wai rashin kuɗi ne ya ke damun sa ba, inda a ka baiyana cewa ra’ayin sa ne kawai ya ji yana don ya je aikin Hajji a keke.

“Na yi ra’ayin tafiya aikin Hajji ne a kan raɗin kai na domin na cika umarnin Ubangiji,” in ji shi.

A duk shekara a na samun tsirarin mutane, musamman a ƙasashen Turai da Gabas ta Tsakiya su je aikin Hajji a ƙafa, keke ko a jirgin ruwa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here