Hajjin 2022: An fara yi wa alhazan Ogun gwaje-gwajen lafiya

0
472

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Ogun ta fara aikin gwaje-gwaje na lafiyar maniyyatan da za su tafi ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin 2022.

Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Salau Dauda ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga maniyyatan, inda ya ce tantancewar wani ɓangare ne na tabbatar da gudanar da aikin Hajji ba tare da matsala ba.

Alhaji Salau ya ce aikin tantancewar na waɗanda su ka biya kuɗin aikin Hajjin da aka yi hasashen za su kai Naira miliyan 2.5 ne.

Inda ya ƙara da cewa waɗanda har yanzu ba su biya kudin ba za a sanar da su nan gaba kaɗan.

Ya kuma umurci alhazai da su baiwa jami’an hukumar hadin kai domin cimma nasarar da ake bukata.

ya gargaɗi alhazan da su gujewa duk wani abu da zai hana su gudanar da aikin Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here