Hajj 2022: Kada ku rabe kujerun Hajji ga ƴan siyasa, IHR ta gargaɗi hukumomin alhazai na jihoh

0
466

Independent Hajj Reporters, IHR, ƙungiya mai zaman kanta da ke sa ido da kawo rahotanni a aikin Hajji da Ummara, ta gargaɗi hukumomin alhazai na jihohi a faɗin ƙasar nan da kada su rabe kaso mafi yawa na kujerun aikin Hajji na bana ga ƴan siyasa da ƴan barandan su.

Ƙungiyar ta gargaɗi hukumomin alhazai na jihohi da kada su bari ƴan siyasa su zare matsa musu lamba a kan su basu kaso mafi tsoka su rabe a junan su.

IHR ta kuma yi kira ga hukumomin akhazai cewa su yi adalci ga maniyyatan da su ka ajiye kuɗaɗen su har shekaru biyu.

Ta ƙara da cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta gindaya wasu sharuɗɗa na rabon kujerun, inda ta yi kira ga hukumomin alhazai na jihohi da su bi waɗannan sharuddan wajen rabon kujerun Hajjin.

IHR ta kuma ci alwashin sa ido a rabon kujerun ga maniyyata a ɗaukacin jihohi 36 na ƙasar nan da Birnin Tarayya.

A tuna cewa ƙasar Saudiyya ta baiwa Nijeriya kuerun Hajji 43,008 a bana, bayan ta dakatar da ibadar na tsawon shekaru biyu sakamakon annobar korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here