Haajjin 2022: Za a fara yi wa alhazan Nassarawa gwajin lafiya ran Laraba

0
541

Hukumar Alhazai Musulmai ta Jihar Nassarawa ta ce ta kammala duk wani shiri na fara yi wa maniyyatan jihar gwaje-gwajen lafiya.

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abdul-Razak Muhammad ya raba wa manema labarai a birnin Lafia.

Sanarwar ta ce tawogar ma’aikatan lafiya, waɗanda a ke sa ran za su yi aikin sau daya a kowacce shiyya, za su fara da shiyyar Nassarawa ta Kudu a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu a shelkwatar hukumarhukumar a titin Jos a Lafiya.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a yi aikin gwaje-gwajen a ranar Alhamis a Nassarawa ta Arewa a Babban Masallacin Juma’a na Akwanga a ranar Alhamis, 19 ga Mayu.

Sai kuma maniyyatan da za a yi wa gwaje-gwajen daga Nasarawa, Udege, Loko, Toto, Umaisha da Gadabuke a Fadar Sarkin Nassarawa a ranar Juma’a, 20 ga Mayu.

Hakazalika maniyyata daga Keffi, Karu, Karshi, Panda, Kokona da Agwada za a yi musu nasu gwaje-gwajen a asibitin sha-ka-tafi na Fadar Sarkin Keffo a ranar Asabar 21 ga wata, da misalin ƙarfe 10 ma safe zuwa 4 na yamma.

Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda basu samu an yi musu ba a kwanakin nan sa iya zuwa shelkwatar hukumarda ke birnin Lafia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here