Hajjin 2022: NAHCON ta ƙaddamar da kwamitin tantance kamfanonin jigilar alhazai

0
223

Yayin da a ke tinkarar Hajjin bana, Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON a yau Litinin ta ƙaddamar da kwamitin tantance kamfanonin jiragen da za su yi jigilar alhazai da na kayayyaki.

Shugaban hukumar, Alhaji Zaikrullah Kunle Hassan ne ya ƙaddamar da kwamitin da ke ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa.

Zikrullah ya hori kwamitin da su tabbata sun bi diddigi wajen tantance takardun kamfanonin domin tabbatar wa sun yi daidai da tsarin sufurin jiragen sama na duniya.

Hajj Reporters ta gano cewa akwai kamfanonin jiragen sama 7 da su ka aika takardun neman sahlewar yin jigilar Alhazai, da su ka haɗa da Max Air, Azman Air, Flynas Air, Arik Air, Med View Airline, Skypower Express, da kuma Westlink Airlines.

Har ila yau Hajj Reporters ta gano cewa kwamitin zai tantance takardun da kamfanonin su ka sabunta a 2020 ne kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here