Hajjin 2022: Saudiya ta hana Alhazai shiga jirgi da zam-zam a jakar hannu

0
491

Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Saudi Arebiya ta fitar da sanarwar hana alhazai shiga jirgi da ruwan zam-zam a jakar hannu yayin barin ƙasar bayan kammala aikin Hajji.

A sanarwar, mai ɗauke da kwanan watan 17 ga watan Mayu, ta hana shiga jirgi yayin barin Saudiya da ga ko wanne filin jirgi na ƙasar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga kamfanonin sufurin jiragen sama da su tabbata sun yi biyayya ga wannan dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here